Zarif Da Mogheni Sun Gana A Taron Birnin Monich A kasar Jamus
Ministan harkokin wajen Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya gana da babbar jami'ar kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar Federica Mogherini a yau a birnin Munich na kasar Jamus, a gefen taron kasa da kasa kan harkokin tsaro na duniya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, Tattaunawar Zarif da Mogherini ta mayar da hankali ne kan alaka tsakanin Iran da kungiyar tarayyar turai, da kuma batun ci gaba da aiki da yarjejeniyar nukiya kan shirin Iran, da kuma yadda bangarorin biyu za su ci gaba da mutunta yarjejeyar bayan ficewar Amurka daga cikinta.
Baya ga haka kuma bangarorin biyu sun duba wani batun wanda ya shafi shirin da kasashen turai suke da shi na yin mu'amala da Iran da suka shafi hada-hadar kudade, domin kaucewa takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar ta Iran.
Federica Mogheni ta jaddada cewam tarayyar turai na nan daram a kan matsayinta na ci gaba da yin aiki tare da Iran da sauran bangarorin da suka ragea cikin yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya.
Shi ma a nasa bangaren Zarif ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniya, matukar sauran bangarorin da ke cikin yarjejeniyar sun ci gaba da mutunta ta.