Sojojin Iran Da Pakistan Na Hadin Guiwar Yaki Da Hare-haren Ta'addanci
(last modified Sun, 24 Feb 2019 09:39:46 GMT )
Feb 24, 2019 09:39 UTC
  • Sojojin Iran Da Pakistan Na Hadin Guiwar Yaki Da Hare-haren Ta'addanci

Sojojin kasar Pakistan sun jaddada azamarsu ta yin aiki tare da kasar Iran domin hana afakuwar wasu hare-haren ta’addanci.

Babban darakta hulda da jama’a na sojojin Pakistan Manjo Janar Asif Ghafoor ne ya bayayna haka a lokacin da yake tsokani akan harin ta’addanci da aka kai a yankin Zaheedan na Iran wanda ya ci rayukan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran da dama.

Manjo janar Asif ya kuma kara da cewa; Kasashen Iran da Pakistan suna da kyakkyawar alaka a tsakaninsu wacce za ta ba da damar yin aiki tare domin karfafa tsaro akan iyakoki.

Jami’in sojan na kasar Pakistan ta kuma ce; Da akwai wasu bangarori da suke son ganin alaka a tsakanin Iran da Pakistan ta gurbata, sannan ya kara da cewa; Ta’addanci yana a matsayin wani kalubale ne mai girma a gaban kasashen yankin.

Da akwai iyaka mai tsawon kilo mita 900 a tsakanin kasashen biyu, don haka Islamabad da Tehran ba za su bari a yi amfani da kasashensu ba domin kai wa kasashunsu hari.