Iran : Jagora Ya Karrama Janar Soleimani, Da Lambar Yabo Mafi Girma Ta Soji
Mar 12, 2019 07:46 UTC
Jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya karrama Janar Ghassem Soleimani, da lambar yabo ta ''Zulfiqar" lambar yabo mafi girma a aikin soji a kasar.
Wannan shi ne karon farko da aka taba baiwa wani jami'in soji a Iran, irin wannan lambar ta yabo tun bayan juyin juya halin musulinci na kasar a 1979.
Janar Soleimani, shi ne babban kwamandan rundinar kare juyin juya halin musulinci a bangaren yaki na ketare, msuamman a yakin da kasar take da 'yan ta'adda na Da'esh a kasashen Siriya da Iraki, wanda hakan ya sanya yana daga cikin mutanen da ake ganin kimarsu da darajarsu a Iran.
A tarihin musulinci ''Zulfiqar" sunan ne da ma'aikin Allah (SAW), ya sanyawa takoba mai baki biyu ta Imam Ali (AS).