Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Ya Fara Ziyarar Aiki A Iran
A safiyar yau ne shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan da takwararsa na Iran Dakta Hasan Ruhani ya tarbe shi a fadar shugaban kasa da ke arewacin birnin Tehran.
Shugaba Zuman wanda yake jagorantar wata babbar tawaga ta mutane 180 da suka hada da 'yan kasuwa da jami'an gwamnati ya iso Tehran din bisa gayyatar da shugaba Ruhanin yayi masa don tattauna batutuwa da suka shafi kasashen biyu da yadda za su kyautata alaka tsakaninsu.
Jim kadan bayan isowar tasa, shugaba Zuma da tawagar tasa sun zauna teburin tattaunawa da shugaba Ruhani da sauran jami'an Iran inda daga karshe dai aka sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi guda takwas na kasuwanci da siyasa da sauransu da nufin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A yayin wannan ziyarar dai shugaba Zuma zai gana da manyan jami'an kasar Iran a kokarin da kasashe biyun suke yi na karfafa alakar da ke tsakaninsu, kamar yadda kuma a ke sa ran zai kai ziyara garin Esfahan daya daga cikin cibiyoyin masana'antu na Iran don gane wa idanuwansa irin ci gaba da Iran ta samu a wannan bangaren.