Mataimakin Kwamandan Dakarun IRGC Na Iran Ya Ja Kunnen Sojojin Kasar Amurka
(last modified Thu, 05 May 2016 05:30:54 GMT )
May 05, 2016 05:30 UTC
  • Mataimakin Kwamandan Dakarun IRGC Na Iran Ya Ja Kunnen Sojojin Kasar Amurka

Na'ibin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) Birgediya Janar Husain Salami ya bayyana cewar Iran ba za ta taba barin jiragen da suke barazana ga tsaronta su wuce ta mashigar ruwar Hurmoz ba, yana mai cewa dakarun na su ba za su taba bari wata kasa ta tsoma baki cikin lamurran da suka shafi tsaron kasar Iran ba.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya bayyana cewar Janar Salami ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar talabijin din kasar ta Iran dangane da wani kudurin doka da majalisar dattawan Amurka ta fitar dangane da tsare-tsaren kariya na Iran musamman dangane da atisayen soji da Iran take gudanarwa a Tekun Fasha inda ya ce yana jan kunnen Amurka da ta tsaya matsayinta kada ta bari wani gigi ya debe ta.

Janar Salami ya kara da cewa muna jan kunnen makiyanmu musamman Amurka da kada su bari gigi ya debe su, su sake tabka kuskuren da suka yi a baya, don kuwa ba za su ji ta dadi ba matukar suka taba mu, yana mai cewa ko shakka babu Iran ba za ta taba bari jirgin ruwan wata kasa da take mata barazana ya wuce ta mashigar Hurmoz ba.

Dangane da batun atisayen soji da dakarun kare juyin suke gudanarwa a Tekun Fashan kuwa, kwamandan na IRGC ya ce su dai sojoji ne da suke da tsare-tsare da atisayensu daidai da bukata, don haka ba za su taba bari wani ya tsoma musu baki cikin hakan ba.