Jagora Ya Zargi Wasu Shugabannin Kasashen Musulmi Da Ha'intarsu
Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar wasu shugabannin kasashen musulmi suna ha'intar al'ummominsu ta hanyar aiwatar da siyasa da manufofin Amurka a kasashen musulmin.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mahalarta gasar karatun Alkur'ani mai girma na kasa da kasa karo na 33 da aka gudanar a birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a jiya Laraba inda yayin da yake nuna bakin cikinsa da yadda wasu kasashen musulmi suka rungumi manyan kasashen duniya ma'abota girman kai maimakon riko da Allah ya bayyana cewar: Ko shakka babu duk wata kasar da take gudanar da siyasar Amurka a yankin nan, to a hakikanin gaskiya ta ha'inci al'ummar musulmi da kuma share fagen tabbatar da ikon Amurka a yankin ne.
Ayatullah Khamenei ya bayyana Amurka a matsayin babbar dagutu kana kuma babbar shaidaniyya don haka ya ce: Babban nauyin da ke wuyan malamai da masana a yau shi ne wayar da kai da bayanin yaudara da kokarin wasa da hankalin al'umma da dawagitai suke yi, sannan kuma wajibi ne su ma al'ummomin kasashen musulmi su yi taka tsantsan kada su fada tarkon yaudarar masu tinkaho da karfi na duniya sannan kuma kada su tsorata da barazanarsu.
Jagoran ya bayyana cewar makiya musulmi suna amfani da dukkanin karfinsu da kuma dukiyar da suke da ita wajen cutar da Musulunci da musulmi, bugu da kari kan kirkiro kungiyoyin takfiriyya masu akidar wahabiyanci da nufin raba kan al'ummar musulmi da shafa musu kashin kaji, sai dai kuma ya ce da yardar Allah ba za su yi nasara a kan al'ummar musulmi din ba.
A shekaran jiya Talata ce aka kawo karshen gasar karatun Alkur'anin na Tehran karo na 33, inda masu karatu da mahaddata Alkur'ani 130 daga kasashe 75 na duniya suka fafata.