Iran, Indiya Da Afghanistan Sun Cimma Yarjejeniyoyin Shige Da Fice A Tsakaninsu
Kasashen Iran, Indiya da Afghanistan sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta bangarori uku da ake kira da yarjejeniyar Chabahar don samar da babbar hanyar yada da zango da kuma hanyoyin sufuri tsakanin kasashen uku.
A yau ne dai aka sanya hannu kan yarjejeniyar a gaban shugabannin kasashen uku, wato Hasan Ruhani na Iran, Ashraf Ghani na Afghanistan da kuma firayi minista Narendra Modi na Indiya wadanda suke ci gaba da ziyarar aiki a nan Iran.
A wata ganawa da yayi da manema labarai jin kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, shugaba Ruhani ya bayyana sanya hannu kan yarjejeniyar a matsayin wani sabon shafi cikin alakar da ke tsakanin kasashe uku.
Shugaba Ruhani ya kara da cewa har ila yau yarjejeniyar wani sako ne na cewa kasashen yankin nan za su iya ciyar da kansu gaba ta hanyar fahimtar juna da aiki tare.
Kafin sanya hannun kan yarjejeniyar, shugaba Ruhanin ya gana da shugabannin biyu wadanda suka iso Iran a lokuta mabanbanta inda suka tattaunawa kan batutuwa daban daban da suka shafi kasashen da ma yankin baki daya.
Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar Indiya Narendra Modi, wanda ya iso Iran tuna yammacin jiya ya ce kasashe ukun za su ci gaba da karfafa alakar da ke tsakaninsu ba wai kawai don amfanin kasashensu ba face ma har da sauran kasashen yankin.
Shi ma a nasa bangaren shugaba Ashraf Ghani na kasar Afghanistan ya bayyana matsayar kasarsa ta ba da himma wajen aganin an cimma nasara cikin wannan yarjejeniyar, yana mai cewa alaka tsakanin kasashen yankin wani lamari ne da zai ciyar da yankin gaba.