Prof. Abdulsharif: Imam Khumaini (r.a) Ya Kasance Gwarzon Hadin Kan Al'ummar Musulmi
Sanannen malamin tarihin nahiyar Afirkan nan dan kasar Zanzibar Farfesa Abdulsharif ya bayyana marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin wani gwarzo da ya ba da rayuwarsa wajen tabbatar da hadin kan musulmi da kuma taimakon marasa galihu da raunanan duniya.
Farfesan Abdulsharif ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da sashen Hausa na gidan radiyon Iran a ci gaba da ziyarar da yake yi a Iran don halartar taron juyayin zagayowar shekaru 27 da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda za a gudanar a gobe Juma'a inda ya ce marigayi Imam Khumaini wani tsayayyen shugaba ne na musulmi mai fadaddiyar zuciya wanda ya riki dukkanin musulmin duniya a matsayin nasa. Shehin malamin ya kara da cewa duk da cewa marigayi Imam ya kasance dan Shi'a ne amma bai takaita tunaninsa ga akidar Shi'anci kawai ba, face dai a ba da dukkanin rayuwarsa wajen ganin ya hada kan musulmi waje guda.
Yayin da yake magana dangane da nasarorin da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya samu a yayin rayuwarsa, Farfesa Abdul Sharif ya ce ko shakka babu Imam ya samu nasara wajen kusato da musulmi waje guda duk kuwa da kokarin da makiya musamman Amurka da wasu kasashen musulmi da aka bar su a baya suka yi na rarraba kan musulmi, kamar yadda kuma ya sanya wa raunanan duniya ruhin tashi wajen neman hakkokinsu da kuma jin cewa lalle su ma za su iya.
Shehin malamin ya nuna tsananin mamaki da farin cikinsa da irin ci gaban da Iran karkashin Jamhuriyar Musulunci inda ya ce kafin ya zo Iran din tunaninsa shi ne zai zo ya ga wata kasa ce wacce ta ci baya ainun sakamakon takunkumi da sauran kafar ungulu da ma'abota girman kan duniya suke mata, don haka ya ce ko shakka babu Iran tana da makoma mai kyau.
A gobe Juma'a ne dai ake sa ran za a gudanar da taron tunawa da shekaru 27 da rasuwar marigayi Imam Khumainin (r.a) a hubbarensa da ke wajen birnin Tehran inda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zai gabatar da jawabi.