Ayat. Kermani: Saudiyya Ta Fada Tarkon Amurka Da Yahudawan Sahyoniya
(last modified Fri, 10 Jun 2016 18:13:01 GMT )
Jun 10, 2016 18:13 UTC
  • Ayat. Kermani: Saudiyya Ta Fada Tarkon Amurka Da Yahudawan Sahyoniya

Na'ibin limamin Juma'ar birnin Tehran Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani yayi kakkausar suka ga siyasar nuna kiyayyar ga al'ummomin yankin Gabas ta tsakiya da Saudiyya ta ke gudanarwa yana mai cewa Saudiyyan ta fada tarkon Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a masallacin juma'ar birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajibi ne a dau darussa daga rayuwar wasu batattun mutane. Don kuwa a halin yanzu kowa yana ganin irin yadda makomar Saudiyya ta kasance duk kuwa kiran kanta da yake yi da sunan mai kula da haramomi guda biyu masu tsarki.

Na'ibin limamin Juma'ar Tehran din ya kara da cewa a halin yanzu kasar Saudiyya ta zama 'yar amshin shatan Amurka da sahyoniya 'yan fashin masallacin Kudus.

Shehin malamin yace a halin yanzu babban aikin da Saudiyya ta sa a gaba shi ne zubar da jinin al'ummar Yemen da kuma goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suna ci gaba da Allah wadai da siyasar kasar Saudiyyan na zubar da jinin al'ummomi da taimakon kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashe daban daban lamarin da ya sanya har Majalisar Dinkin Duniya sanya ta cikin kasashen da suke take hakkokin kananan yara, duk da cewa ta yi amfani da matsin lamba da kudi wajen tilasta wa babban sakataren MDD Ban Ki Moon cire ta daga cikin jerin wadannan kasashen kamar yadda shi da kansa ya tabbatar da hakan.