Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Wani Shirin Kai Hare-Haren Ta'addanci Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i6979-jami'an_tsaron_iran_sun_dakile_wani_shirin_kai_hare_haren_ta'addanci_kasar
Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta sanar da samun nasarar dakile wani kokari da 'yan ta'adda suka yi na kai hare-hare birnin Tehran da wasu biranen kasar cikin watan Ramalana, inda suka kama wani adadi na 'yan ta'addan.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 20, 2016 06:34 UTC
  • Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Wani Shirin Kai Hare-Haren Ta'addanci Kasar

Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta sanar da samun nasarar dakile wani kokari da 'yan ta'adda suka yi na kai hare-hare birnin Tehran da wasu biranen kasar cikin watan Ramalana, inda suka kama wani adadi na 'yan ta'addan.

Kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) ya bayyana cewar cikin wata sanarwa da Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirrin ta fitar a yau din nan Litinin ta ce jami'anta sun sami nasarar ganowa da kuma dakile kokarin da wasu 'yan kungiyoyin ta'addanci masu kafirta musulmi suka yi na tada bama-bama da tayar da su a biranen Tehran da wasu manyan biranen kasar .

Sanarwar ta kara da cewa jami'an tsaron sun sami nasarar kama wasu daga cikin 'yan ta'addan da suke shirin tayar da bama-baman a wajajen tarurruka na addini a cikin watan Ramalana, inda suka same su da wani adadi mai yawa na ababe masu fashewa.

Ma'aikatar ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda aka kama din kuma a nan gaba za a sanar da al'umma halin da ake ciki dangane da wannan shiri na ta'addanci da aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin mafiya girma da munin makirci da kuma ta'addancin da aka so yi a kasar.