Wilayati Yana Ziyara A Kasar Rasha
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i82-wilayati_yana_ziyara_a_kasar_rasha
Shugaban Cibiyar Bincike da nazari na majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci a Iran ya ce; Mahangar Tehran da Moscow dangane da rikicin Syria ta yi daidai.
(last modified 2018-08-22T06:57:44+00:00 )
Feb 01, 2016 14:22 UTC
  • Wilayati Yana Ziyara A Kasar Rasha

Shugaban Cibiyar Bincike da nazari na majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci a Iran ya ce; Mahangar Tehran da Moscow dangane da rikicin Syria ta yi daidai.

Ali Akbar wilayati wanda ya ke ziyarar aiki a kasar Rasha ya kara da cewa; A yayin ganawarsa da mahukuntan kasar, batun kasar Syria na daga cikin muhimman batutuwan da za su tattauna.

Ali Akbar Wilayati ya kuma ci gaba da cewa; Alakar kasashen Iran da kuma Rasha a wanann lokacin na tarihi ta bunkasa fiye da kowane lokaci a baya, ta kuma shafi bangarori daban-daban da su ka hada da tsaro.

Har ila yau, Ali Akbar Wilayati ya ce; Da akwai daidaiton tunani tsakanin kasashen biyu dangane da kasar Syria sannan kuma da rashin yarda da tsoma bakin da kasashen waje su ke yi a ciki.

A yau litinin ne dai, Ali Akbar Wilayati ya isa kasar Rasha domin ganawa da jami'an gwamnatin kasar.