Larijani: Kafa Majalisar Shugabancin Kasar Yemen Babban Ci Gaba Ne
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i9688-larijani_kafa_majalisar_shugabancin_kasar_yemen_babban_ci_gaba_ne
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Lrijani ya yaba da kafa majalisar shugabancin kasar Yemen da bangarorin siyasar kasar suka yi domin tafiyar da kasar na wucin gadi.
(last modified 2019-03-18T02:12:56+00:00 )
Aug 15, 2016 08:57 UTC
  • Larijani: Kafa Majalisar Shugabancin Kasar Yemen Babban Ci Gaba Ne

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Lrijani ya yaba da kafa majalisar shugabancin kasar Yemen da bangarorin siyasar kasar suka yi domin tafiyar da kasar na wucin gadi.

Kamfanin dillancin labaran Iskna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yau a gaban majalisar dokokin kasar Iran a Tehran, shugaban majalisar Ali Larijani ya bayyana kafa majalisar shugabancin kasar Yemen da cewa zai taimaka matuka wajen warware lamurra da dama a kasar.

Larijaniya ce fiye da shekara guda kenan da jiragen yakin Saudiyya da na wasu kasashen da ta dauka haya suke lugudan wuuta kan kan fararen hula a Yemen, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar dubbai daga cikin fararen hula da suka hada da mata da kanan yara, ba tare da duniya ta iya daukar matakin taka wa Saudiyya birki ba.