Iraki : Za'a Iya Kwato Mosul Kafin Karshen Shekara Nan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10366-iraki_za'a_iya_kwato_mosul_kafin_karshen_shekara_nan
Babban kwamadan sojojin A murka a yankin gabas ta tsakiya ya bayyana cewa aikin kwato birnin Mosul daga hannun 'yan ta'adda na IS zai iya kaiwa har zuwa karshen shekara nan da muke ciki.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 30, 2016 12:52 UTC
  • Iraki : Za'a Iya Kwato Mosul Kafin Karshen Shekara Nan

Babban kwamadan sojojin A murka a yankin gabas ta tsakiya ya bayyana cewa aikin kwato birnin Mosul daga hannun 'yan ta'adda na IS zai iya kaiwa har zuwa karshen shekara nan da muke ciki.

Da yake magana a wani taron manema labarai  a ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagone, Janar Joe Votel ya ce gurin da firaministan Iraki Haider al-Abadi yake dashi na ganin an kwato birnin na Mosul daga hannun 'yan ta'addan kafin karshen wannan shekara, a nawa gani zamu iya cimma wannan gurin.

Saidai Janar din ya yi  gargadin cewa za'a gwabza fada mai tsanani kafin kwato birnin dake zamen na biyu a wannan kasa ta Iraki.

Kuma a cewarsa a cikin irin kalunalen da za'a cin karo dasu wajen neman kwato birnin, shi ne 'cewa yan ta'addan zasu iya amfani da munanen hanyoyi da suka hada da nakiyoyi da abubuwa masu fashewa don haka tarkuna a cikin birnin kana zasu ma iya garkuwa da fararen hula don haka fadan zai yi muni sosai.