Syria: Sojojin Gwamnati Suna Ci gaba da Samun Nasara Akan 'Yan'tadda
Majiyar Sojojin Syria ta tabbatar da cewa; suna samun galaba akan 'yan ta'adda a yankunan kasar daban-daban.
Tashar telbijin din al-alam ta watsa labarun da ke cewa; Sojojin Kasar ta Syria sun ka hari akan ayarin motocin yan ta'adda a garin Dar'ah da yankin al-bajabijah tare da kashe 7 daga cikinsu da kuma jikkata wasu.
A kudancin gundumar Halab kuwa sojojin na Syria sun masu ci gaba a jami'ar tsaro ta soja da ke hannun 'yan ta'adda. A cikin garin na Halab, sojojin na Syria sun kai hari da manyan bindigogi a cikin sansanonin 'yan ta'adda. Ana sa ran cewa nan da wasu sa'aoi za su kori 'yan ta'addar daga wani muhimmin yanki da ke hannun 'yan ta'addar.
A Kudancin Halab, da ke arewacin kasar kuwa an sami sabani a tsakanin kungiyoyin na 'yan ta'adda, bayan da wasu daga cikinsu su ka janye daga filin daga, wasu kuma su ka zarge su da cin amana.