Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Yi Nasarar Kashe 'Yan Ta'adda Kimanin 100
Sojojin gwamnatin Siriya da dakarun sa-kai sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda kimanin 100 a yankunan garuruwan Halab da Hamah da suke arewacin kasar.
A wani gumurzu da aka gudanar tsakanin sojojin gwamnatin Siriya da suke samun taimakon dakarun sa-kai da kuma gungun 'yan ta'adda a yankunan garuruwan Halab da Hamah da suke shiyar arewacin kasar a jiya Litinin gungun 'yan ta'adda kimanin 100 ne suka bakonci lahira tare da tarwatsa jerin motocinsu na yaki.
A gefe guda kuma yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren wuce gona da iri da mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish suka kai ta hanyar kunan bakin wake da tarwatsa mota da suka cika ta da bama -bamai a yankunan garin Tartus na kasar ta Siriya a jiya Litinin sun haura zuwa 30 tare da jikkatan wasu kimanin 45 na daban.