Jakadan Siriya A MDD: Rikicin Siriya Ba Yakin Basasa Ba Ne
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10708-jakadan_siriya_a_mdd_rikicin_siriya_ba_yakin_basasa_ba_ne
Jakadan kasar Siriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Dakta Bashar al-Ja'afari ya bayyana cewar rikicin da ke faruwa a kasar Siriyan ba yakin basasa ba ne, face dai wani makirci ne aka shirya wa kasar ta hanyar shigo da dubban 'yan ta'adda cikin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 07, 2016 01:25 UTC
  • Jakadan Siriya A MDD: Rikicin Siriya Ba Yakin Basasa Ba Ne

Jakadan kasar Siriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Dakta Bashar al-Ja'afari ya bayyana cewar rikicin da ke faruwa a kasar Siriyan ba yakin basasa ba ne, face dai wani makirci ne aka shirya wa kasar ta hanyar shigo da dubban 'yan ta'adda cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya bayyana cewar Dakta Ja'afarin ya bayyana hakan ne a jiya Talata a birnin New York, helkwatar MDDn inda ya ce: Ba za a iya kiran abin da ke faruwa a kasar Siriya da cewa yakin basasa ne ba, don kuwa dubun dubatan 'yan ta'adda daga sama da kasashe 100 ne aka shigo da su kasar karkashin kulawar wasu kasashen da ke makwabtaka da Siriya da nufin dagula lamurra a kasar.

Jakadan Siriyan a MDD ya ci gaba da cewa: Tabbas gwamnatin Siriya za ta ci gaba da sauke nauyin da ke wuyanta na kare iko da hadin kan kasar bugu da kari kan tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ga dukkanin 'yan kasar da kuma ci gaba da fada da duk wani dan ta'addan da ya daga makami da nufin yakar gwamnati da kuma  al'ummar Siriyan.

Dakta Bashar al-Ja'afari dai yana mayar da martani da kokarin da wasu suke yi da bayyanar abin da ke faruwa a kasar Siriya a matsayin wani yaki ne na basasa tsakanin 'yan kasar masu adawa da yadda gwamnatin kasar take gudanar da ikonta da kuma gwamnatin wacce take kokarin tabbatar da ikon nata a kan al'umma da karfin tuwo don rufe hakikanin hannun da wasu kasashen larabawa musamman Saudiyya suke da shi wajen shigo da 'yan ta'adda Siriyan.