An hallaka wasu Komondojin 'yan ta'adda A Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10816-an_hallaka_wasu_komondojin_'yan_ta'adda_a_siriya
Wasu komondojin 'yan ta'adda a gefen garin halab dake arewa maso yammacin Siriya sun hallaka
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 09, 2016 06:18 UTC
  • An hallaka wasu Komondojin 'yan ta'adda A Siriya

Wasu komondojin 'yan ta'adda a gefen garin halab dake arewa maso yammacin Siriya sun hallaka

Kafar watsa labaran Al-Ahad ta kasar Labnon ta habarta cewa hare-haren da jiragen yakin kasar Siriya suka kai a yammacin garin Halab a daren jiya Alkhamis ya yi sanadiyar hallakar wasu Komondojin kungiyoyin 'yan ta'adda na Kungiyar Jabhatul-Nusra da Jaishul-Fatah, daga cikin su a kwai Usama Namura da ake kira da Abu Hajir Alhumsa komandan dake kula da bangaren sojoji na kungiyar Jabhatu-Nusra.da kuma Abu Umar Sarakib daya daga cikin shugabanin kungiyar 'yan ta'addar Jaishul-Fatah da kuma wasu 'yan ta'adda da dama.

A wani Labari na daban, Sojojin Siriya sun fatattaki 'yan ta'adda a yankin Ramusa dake gabashin garin na Halab, inda a yanzu suke rike da ikon yankin.har ila yau Sojojin na Siriya su kwace iko da yankin Humat daga hanun 'yan ta'adda.