Siriya : Assad Ya Bayyana A Yayin Idin Sallah Babba
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10924-siriya_assad_ya_bayyana_a_yayin_idin_sallah_babba
Shugaba Bashar Al Asad na Siriya ya bayyana a fili a yayin sallar idin babbar sallah a wabi masalaci dake lardin Daraya a kusa da Birnin Damascos.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 12, 2016 04:55 UTC
  • Siriya : Assad Ya Bayyana A Yayin Idin Sallah Babba

Shugaba Bashar Al Asad na Siriya ya bayyana a fili a yayin sallar idin babbar sallah a wabi masalaci dake lardin Daraya a kusa da Birnin Damascos.

kafofin yada labarai daga kasar sun nuno Assad a cikin jerin masalata dake idin babbar Sallah a daura da mayan malumai na kasar da kuma jami'an gwamnati a cikin masalacin Sada ibn Moaz dake Daraya.

Garin Daraya, dai shi ne tushen borin kyammar gwamnatin Bashar Al'Assad da wasu 'yan kasar keyi, kuma a karshen watan Agusta ne dakarun kasar suka kwace shi daga hannun 'yan tawaye.

A hannu daya babban malamin birnin Damascos Adnane al-Afyouni daya jagoranci sallah idi ya ce ya kamata Daraya ta zama misali na hadin kan al'umma da kuma kawo karshen yaki a kasar.

Alkaluma sun nuna cewa mutane sama da 290.000 ne suka rasa rayukansu a yakin da aka kwashe shekaru biyar ana yi a wannan kasa ta Siriya.