Iraki:Komawa 'yan hijra zuwa garin Karkuk
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10948-iraki_komawa_'yan_hijra_zuwa_garin_karkuk
Dariruwan iyalan Iraki da hare-haren ta'addanci na Kungiyar IS ya raba da mahalinsu a yankunan dake kalkashin ikon karkuk. su suka koma cikin garin na Karkuk.
(last modified 2018-08-22T06:58:55+00:00 )
Sep 13, 2016 00:41 UTC
  • Iraki:Komawa 'yan hijra zuwa garin Karkuk

Dariruwan iyalan Iraki da hare-haren ta'addanci na Kungiyar IS ya raba da mahalinsu a yankunan dake kalkashin ikon karkuk. su suka koma cikin garin na Karkuk.

Majiyar watsa labaran kasar Iraki ta habarta cewa a jiya Litinin Kimanin 'yan gudun hijrar Iraki dubu guda ne da hare-haren ta'addancin IS ya raba da gidajen su a yankin Hawija mai nisan kilomita 55 daga kudu masu yammacin Karkuk, suka isa garin na Karkuk, kuma mafi yawa daga cikin su Mata, yara kanana gami da masu yawan shekaru ne.

A yayin da suke gudun  wani Bam ya tashi a kan hanyar su na zuwa birnin Karkuk din, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 9 tare da jikkata wasu 6 na daban. ko baya ga hakan, kungiyar ta'addancin IS ta yi gaba da wasu fararen hula 15 kan zarkin su da taimakawa mutane wajen gudu daga yankunan dake kalkashin ikon su na Hawuja.

Ya zuwa yanzu fararen hula da dama ne kungiyar ta IS ta kashe kan zarkinsu da kokarin gudu daga cikin garin na Hawija. Garin Hawija dai na a kudu maso yammacin jihar Karkuk kuma yankunan dake kewaye da shi kamar su Rasha, Riyyad da Za'ab, daga shekarar 2014 zuwa yanzu na kalkashin mamayar kungiyar IS, inda suke ci gaba da karkuwa da fararen hula.