'Yan ta'adda Sun Yi Asara Mai Yawa A Kasar Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11131-'yan_ta'adda_sun_yi_asara_mai_yawa_a_kasar_syria
Sojojin Syria Sun kashe 'yan ta'adda da dama a yankunan Qunaidhara da kuma Dar'ah.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 16, 2016 14:28 UTC
  •  'Yan ta'adda Sun Yi Asara Mai Yawa A Kasar Syria

Sojojin Syria Sun kashe 'yan ta'adda da dama a yankunan Qunaidhara da kuma Dar'ah.

Tashar telbijin din al'alam daga kasar Syria, ta nakalto cewa; Sojojin Syria sun kashe 'yan ta'adda  masu yawa a yankunan Dar'ah da kuma Qunaidharah da adadinsu ya kai 500 a cikin kwanaki uku ajere. Bugu da kari, a tsakanin wadanda aka kashe shin da akwai kwamandojin kungiyoyin 'yan ta'adda 20.

Har ila yau, rahoton ya ci gaba da cewa; 'yan sahayoniya sun dauki 'yan ta'adda 80 da su ka jikkata domin yi musu magani.

A yau juma'a ma, sojojin syria din sun kashe wasu 'yan ta'addar da su ke kai 15 a yankin na Qunaidhara.