Iraki : An Kori Ministan Kudi
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11359-iraki_an_kori_ministan_kudi
Majalisar dokokin Iraki ta kada kuri'ar tsige ministan kudin kasar, Hoshyar Zebari daga kan mukaminsa, bisa zarge-zargen cin hanci.
(last modified 2018-08-22T06:58:57+00:00 )
Sep 21, 2016 12:40 UTC
  • Tsohin ministan kudi na Iraki, Hoshyar Zebari
    Tsohin ministan kudi na Iraki, Hoshyar Zebari

Majalisar dokokin Iraki ta kada kuri'ar tsige ministan kudin kasar, Hoshyar Zebari daga kan mukaminsa, bisa zarge-zargen cin hanci.

Daga cikin 'yan majalisu 249 da majalisar ta kunssa 158 ne suka amunce da tsige Mr Zebari dake rikeda mukamin  tun cikin shekara 2014. 

M. Zebari sanannen dan siyasa ne a wannan kasa ta Iraki, kuma a cen baya ya rike mukamin ministan harkokin waje na tsawon shekaru da dama.

Korar Mista Zebari na zuwa a daidai lokacin da kasar ke cikin tsaka mai wuya a fannin tattalin arziki mai nasaba da faduwar farashin man fetur de kuam yakin da kasar keyi da kungiyar 'yan ta'addan (IS).

A watan Agusta dai Mista Zebari ya fuskanci tambayoyi kan wannan badakala ta cin hanci, inda ya yi watsi da zarge zargen.

A ranar 25 ga watan Agustan daya gabata takwaransa na tsaro ne, Khalid al-Obeidi majalisar ta kora bisa irin wannan zargin.

A watan Yulin daya gabata ministan cikin gidan kasar ne, Mohammed al-Ghabban, ya yi murabus sakamakon mumunan harin da kungiyar IS ta kai wanda yayi sanadin mutuwar mutane sama da 300.

Ko baya ga hakan firaministan kasar haidar Al-Abadi ya shaida cewa ya amunce da murabus din wasu ministoci shida a cikin 'yan watannin nan.