Siriya : Rasha Ta Sake Musunta Kai Hari Kan Ayarin Motocin Agaji
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11362-siriya_rasha_ta_sake_musunta_kai_hari_kan_ayarin_motocin_agaji
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar cewa akwai wani jirgi mara dreba na kawacen da Amurka ke jagoranta da yake a wurin da aka kai hari kan ayarin motocin dake dauke da kayan agaji zuwa Aleppo.
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 21, 2016 13:15 UTC
  • Siriya : Rasha Ta Sake Musunta Kai Hari Kan Ayarin Motocin Agaji

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar cewa akwai wani jirgi mara dreba na kawacen da Amurka ke jagoranta da yake a wurin da aka kai hari kan ayarin motocin dake dauke da kayan agaji zuwa Aleppo.

Sanarwar ta ce mintina kadan kafin motocin su kama da wuta jirgi mara matuki ya kusa kai a yankin Orum al-Koubra, kafin daga bisani ya fito wurin bayan mintina talatin.

Wannan bayanin ya fito ta bakin kakakin ma'aikatar tsaron Rasha Janar  Igor Konachenkov a lokacinda yake sake musunta zargin kasarsa da kai hari kan ayarin motocin a kusa birnin Aleppo na kasar Siriya.

Yau Laraba ne kwamitin sulhu na MDD ke zama na musamman kan halin da ake ciki a Syria, wanda sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ke halarta.