Sojojin Syria sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Halab
"Yan ta'adda a kudancin Halab na Syria sun sha kashi.
Tashar telbijin din al'alam mai watsa shirye-shiryenta daga nan Iran, ya ce; Sojojin Syria tare da taimakon abokan kawancensu sun kai munanan hare-hare akan 'yan ta'adda da su ke rike da hanyar al-amuriyya zuwa Ramusa da ke kudancin yankin Halab, tare da kwance iko da yankin daga hannunsu.
Sojojin na Syria sun yi amfani da makamai daban-daban matsakaita da manya wajen kai farmakin akan 'yan ta'addar.
Bugu da kari, jiragen yakin na Syria da na Rasha sun jefa bama-bamai akan sansanonin 'yan ta'addar da yankin na amuriyyah da al-shukriyya da sheikh Sa'id da Butanul-Qasr da Kilasha da su ke a gabacin Halab.
'Yan ta'adda da dama ne su ka halaka tare kuma da korarsu daga yankunan da su ke rike da su.