Kungiyar Da'ish Ta Kashe Babban Kwamandanta Abu-Hamza Al-Libiy
Kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta zartar da hukuncin kisa kan daya daga cikin manyan kwamandojinta mai suna Abu-Hamza Al-Libiy da mukarrabansa 16 a garin Mosel na kasar Iraki.
Tashar talabijin na Rusiyal – Yaum ta kasar Rasha ta watsa rahoton cewa: Kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta zartar da hukuncin kisa kan daya daga cikin manyan kwamandojinta a yankin kudancin garin Mosel mai suna Abu-Hamza Al-Libiy da mukarrabansa 16 kan laifin gudu a filin yaki a lokacin da sojojin gwamnatin Iraki suka yi dirar mikiya kan yankin Al-Qadah da ke kudancin garin Mosel.
Kungiyar ta Da'ish ta kashe Abu-Hamza Al-Libiy da mukarrabansa 16 ne ta hanyar kona su da wuta a bainar jama'a a yankin Ghabat da ke garin na Mosel.
Sojojin gwamnatin Iraki da dakarun sa-kai na kasar dai sun yi nasarar 'yantar da yankin na Al-Qadah Al-Sharqat daga mamayar 'yan ta'addan Da'ish.