Iraki : Bam Ya Kashe Mutane 7 A Masallaci
Sep 30, 2016 07:24 UTC
Rahotannin daga Irakin na cewa wani harin kunar bakin wake da ka kai da mota ya kashe mutane akalla bakwai a lokacin da suke gudanar da sallah Juma'a a lardin Madaen.
ko baya ga wadanda suka riga mu gidan gaskia akwai wasu da dama da suka jikkata a cewar rahotannin.
An dai kai harin ne yau Juma'a a lardin Madaen dake kudancin Bagadaza babban birnin kasar.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da 'yan ta'adda masu ikirari da sunnan musulinci ke kai hari kan masallata a wannan kasa.
ko a ranar Talata data gabata an kai hare-hare har guda uku a yankin gabas da kudu na Bagadaza inda mutane kimanin 20 suka mutu, kana wasu kusan arba'in suka raunana.
Tags