Iraki: Zaluncin Da'esh ta ke yi ya kusa zuwa karshe.
Oct 04, 2016 15:28 UTC
Karshen Da'esh ya karato A kasar iraki
Pira ministan kasar Iraki ya bayyana cewa; An kusa zuwa lokacin da Iraki za ta zama 'yantacciya daga kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh.
Haydar Abadi da ya aikewa mutanen Mosel sako a yau talata ya ce; Kamar yadda aka daga tutar Iraki, a cikin yankunan al-sharqad, da alqiyarah, to ba da jimawa ba, za a daga tutur a birnin Mosel.
Bugu da kari, Pira ministan na kasar Iraki ya kira yi mutanen Mosle da su baiwa sojojin kasar hadin kai a yayin da za su fara kai farmaki.
Tare da cewa Pira ministan kasar ta Iraki bai bayyana ranar da za a fara kai hari a Mosel ba, sai dai kafafen watsa labarun kasar suna hasashen cewa ba da jimawa ba ne za a fara kai harin.
Tags