Sojojin Gwamnatin Iraki Sun Halaka 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Masu Yawa
Sojojin gwamnatin Iraki da dakarun sa-kai sun halaka wasu gungun 'yan ta'adda tare da yantar da yankuna da dama a garin Mosel na kasar.
Makiyar rundunar sojin Iraki a jiya Talata ta sanar da halakar wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish ciki har da Ibrahim Muhammad Hail da ake masa lakabi da Abu-Sulaiman babban kusa a kungiyar a yankunan garin Mosel da ke arewacin kasar ta Iraki.
Sojojin Iraki da dakarun sa-kan sun yi dirar mikiya ce kan gungun 'yan ta'addan, inda suka kashe nafi yawansu tare da jikkata wasu adadi mai yawa a sassa daban daban na garin na Mosel.
Har ila yau sojojin gwamnatin Iraki da taimakon dakarun sa- kai sun 'yantar da yankuna da dama daga mamayar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish ciki har da yankin Dara'bashah da ke arewacin garin Ramadi tare da murkushe 'yan ta'addan da suka ki arcewa saboda da tsoron fuskantar kisan wulakanci daga takwarorinsu.
Kungiyar ta'addanci ta Da'ish dai tana zartar da hukuncin kisa gilla ta wulakanci kan mabiyanta matukar suka tsere daga filin daga kuma komai uzurunsu, inda a cikin 'yan kwanakin nan kungiyar ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar kona mambobinta da wuta a kasar Siriya kan laifin gudu daga filin yaki bayan da sojojin Siriya suka fi karfinsu.