Siriya : Sojoji Sun Rage Kai Farmaki A Halep
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i12040-siriya_sojoji_sun_rage_kai_farmaki_a_halep
Rundinar sojin kasar Siriya ta sanar da rage kai hare-harenta a birnin Halep, bayan shafe makwanni biyu na kai farmaki ba kakkautawa a wannan yankin.
(last modified 2018-08-22T06:59:02+00:00 )
Oct 06, 2016 02:23 UTC
  • Siriya : Sojoji Sun Rage Kai Farmaki A Halep

Rundinar sojin kasar Siriya ta sanar da rage kai hare-harenta a birnin Halep, bayan shafe makwanni biyu na kai farmaki ba kakkautawa a wannan yankin.

Wata sanarwa daga rundunar ta ce bayan nasara da sojojin suka yi a Halep, za'a rage kai hare-hare ta sama da kuma kasa domin baiwa fararen hula dake bukata ficewa daga birnin dama.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da duniya ke neman hanyoyin diflomatsiya domin samar da hanyoyin warware rikicin kasar.

A wani lokaci yau Alhamis ne ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Faransa,Jean-Marc Ayrault, zai isa birnin Moscow na Rasha da nufin cimma wani kudirin kwamitin tsaro na MDD na sake tsagaita wuta a Halep.

A ranar Litinin data gabata ce Amurka ta sanar da dakatar da tattaunawar da take da Moscow akan farfado da yarjejeniyar ta tsagaita wuta a Halep.