Bukatar kasar Turkiya na fitar kasar Turkiya daga Kasar Iraki
Babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa ya bukaci kasar Turkiya da ta mutunta kasar Iraki.
A wata sanarwa da ya fitar a wannan Alkhamis, Babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Abu Gaiz ya bukaci magabatan kasar Turkiya da su mutunta kasar iraki, kuma su kuji duk wani aiki ko maganganu da za su kara rura wutar rikici a tsakanin kasashen biyu.kafin hakan dai, kakakin kungiyar kasashen Larabawa Mahmud Afifi ya ce kungiyar ta damu matuka kan rikicin dake faruwa tsakanin kasashen Turkiya da Iraki sannan kuma ya ce kungiyar tana kyakkyawan fata kancewa kudurin da ta dauka a babban taron ta da ta gudanar a birnin Nuwaktchot babban birnin kasar Murtaniya ranar 8 ga watan Satumbar da ya gabata zai kawo karshen wannan rikici.
A yayin taron kungiyar kasashen Larabawan, Ibrahim Ja'afari Ministan harakokin wajen Iraki tare da tawagar dake rufa masa baya sun bukaci kungiyar da ta dauki wani kudiri da zai matsa lamba ga kasar Turkiya a kan ta janye Dakarunta daga cikin kasar ta Iraki.
A karshen shekarar 2015 ne kasar Turkiya ta jibke dariruwan Sojojin ta a sansanin Ba'ashika dake arewacin Mosil a Jihar Nainuwa na kasar Iraki a kan da'awar yaki da ta'addanci.
Duk da cewa kasar ta Iraki ta kai karar turkiyan gaban kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da kwamitin tsaro na MDD, to amma har yanzu magabatan birnin Ankara ba su janye sojojin na su ba daga cikin kasar Irakin.