Amnesty International Ta Nuna Damuwarta Kan Hare-Haren Turkiya Cikin Siriya
(last modified Thu, 25 Feb 2016 06:25:19 GMT )
Feb 25, 2016 06:25 UTC
  • Amnesty International Ta Nuna Damuwarta Kan Hare-Haren Turkiya Cikin Siriya

Kungiyar kare hakkokin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bayyana tsananin damuwarta dangane da hare-haren da sojojin kasar Turkiyya suke kai wa cikin kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran Intertax ta kasar Rasha ya jiyo Tirana Hassan, daya daga cikin manyan jami'an kungiyar Amnesty International din, yana fadin cewa kungiyar ta damu ainun dangane da ci gaba da hare-haren da sojojin Turkiyyan suke kai wa cikin kasar Siriyan wanda yana iya shafan fararen hula.

A jiya laraba ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta bukaci cibiyoyin kasa da kasa da su dau matakan da suka dace wajen kawo karshen hare-haren da sojojin Turkiyyan suke kai wa cikin kasar Siriya da sunan hana 'yan kungiyar Kurdawan Siriya kusato kan iyakar kasar, lamarin da kasashen duniya daban-daban suka yi Allah wadai da shi.