Kashe Jami'an Tsaron Afganistan Fiye Da 200 A Lardin Helmand
(last modified Sat, 15 Oct 2016 06:19:16 GMT )
Oct 15, 2016 06:19 UTC
  • Kashe Jami'an Tsaron Afganistan Fiye Da 200 A Lardin Helmand

Jami'an tsaron Afganistan fiye da 200 ne suka rasa rayukansu a dauki ba dadin da suka yi da mayakan kungiyar Taliban a lardin Helmand na kasar.

Mataimakin shugaban Majalisar lardin Helmand Abdul-Majid Akhoun-Zadeh ya sanar da cewa: A dauki ba dadin da aka yi kwanaki goma da suka gabata tsakanin jami'an tsaron Afganistan da 'yan ta'addan kungiyar Taliban a yankunan da suke lardin Helmand jami'an tsaron kasar fiye da 200 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 100 na daban suka samu raunuka.

Abdul-Majid ya kara da cewa: Dauki ba dadin ya lashe rayukan fararen hula da yawansu ya kai kimanin 45.

Majiyar tsaron lardin na Helmand ta sanar da cewa: A halin yanzu haka an tura jami'an tsaro na musamman 300 zuwa yankunan lardin na Helmand da nufin taka burki wa kutsen 'yan kungiyar ta Taliban.