Bam ya tashi a birnin Bagdaza na kasar Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i12523-bam_ya_tashi_a_birnin_bagdaza_na_kasar_iraki
Harin ta'addanci ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula biyu tare da jikkata wasu 4 na daban.
(last modified 2018-08-22T06:59:05+00:00 )
Oct 16, 2016 09:03 UTC
  • Bam ya tashi a birnin Bagdaza na kasar Iraki

Harin ta'addanci ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula biyu tare da jikkata wasu 4 na daban.

Rahotani dake fitowa daga kasar Iraki sun tabbatar da tashin Bam a anguwar Kadisiya dake tsakiyar garin Bagdaza, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula biyu tare da jikkata wasu 4 na daban.

A bangare guda Majiyar tsaron kasar ta sanar da cewa Jiragen yakin saman kasar sun kai hari a wuraren 'yan ta'addar IS dake yammacin garin Ramadi na jihar Anbar, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka 'yan ta'adda 13 tare da lalata wasu daga cikin motocin su.,wannan hari na zuwa ne a yayin da 'yan ta'addar ke kokarin kai wa Sojojin Irakin hari a kan hanyar su ta garin Biji zuwa Hadisa, lamarin da ya yi sanadiyar dakile ta'addancin.

A gefe guda Rundunar hadin gwiwar da aka kafa don 'yanto garin Mosil ta sanar da fara kai hare- hare kan 'yan ta'addar a birnin na Mosil