Iraki : Yunkurin Ceto Mosul Na Gamuwa Da Cikas
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i12766-iraki_yunkurin_ceto_mosul_na_gamuwa_da_cikas
Hare haren kunar bakin wake da 'yan ta'addan IS ke kaiwa a yankin KIrkuk na Iraki na maida hannun agogo baya a yunkurin kwato birnin Mosul.
(last modified 2018-08-22T06:59:07+00:00 )
Oct 22, 2016 02:46 UTC
  • Iraki : Yunkurin Ceto Mosul Na Gamuwa Da Cikas

Hare haren kunar bakin wake da 'yan ta'addan IS ke kaiwa a yankin KIrkuk na Iraki na maida hannun agogo baya a yunkurin kwato birnin Mosul.

Kimanin mutane 22 ne aka rawauto sun rasa rayukansu a hare haren kunar bakin wake da kuma fadan da ake gwabza da 'yan ta'addan na IS a birnin Kirkuk.

Ana dai kyallon wannan salon na IS a mastayin wani salo na raba hankalin a daidai lokacin da ake kai masu farmaki a Mosul birni na biyu mafi girma a Iraki.

A farkon wannan makon ne dai dakarun Iraki hadin gwiwa da mayakan sa kai na 'yan Shi'a tare da tallafin jiragen saman yakin kawacen da Amurka ke jagoranta suka soma kai wani gagarimun farmaki a birnin Mosul da nufin sake kwato shi daga hannun 'yan ta'addan na IS.