Venezuela : 'Yan Adawa Sun yi Kiran Zanga-zanga
Oct 22, 2016 06:16 UTC
'Yan adawa a kasar Venezuela sun yi kiran wata gagarimar zanga zanga a ranar laraba mai zuwa domin nuna fishinsu akan matakin dakatar da shirin zaben jin ra'ayin jama'a.
Hukumar shirya zaben kasar ce, ta dakatar da shirin na kokarin ganin an kawo karshen gwamnatin shugaban kasar Nicolas Maduro.
‘Yan adawan kasar dai na fafutukar ganin shugaba Maduro ya sauka daga mukaminsa, saboda a cewarsu ya gaza wajen warware matsalar tattalin arzikin kasar.
Matakin dakatar da shirya kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya zo ne bayan haramta sanya hannun da miliyoyin ‘yan adawa a Venezuela suka yi.
Tags