Sojojin Iraki Sun ci Gaba Da Samun Nasara Akan "Yan ta'adda.
Oct 22, 2016 15:28 UTC
Sojojin Iraki Suna Fada Da Da'esh A Kirkuk
Jami'an tsaron Kasar Iraki suna ci gaba da fada 'yan ta'adda a birnin Kirkuk a rana ta biyu a jere.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya nakalto cewa; Har yanzu mayakan na Da'esh, suna cikin birnin, musamman 'yan kunar bakin wake, da kuma maharba.
Rundunar fada da ta'addanci ta Iraki, wacce ta shiga birnin tana ci gaba da farautar 'yan ta'addar acikin gine-gine da lunguna.
Kawo ya zuwa yanzu ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Iraki, ta ce an kashe jami'an tsaro 46 da jikkata 133 a fada da 'yan ta'addar.
Babban jami'in 'yan sandan birnin Kirkuku ya ce adadin 'yan ta'addar da aka kashe sun kai 48.
Tags