Iraki : MDD Zata Karbi Masu Gujewa Fadan Mosul 150,000
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce a shirye take domin karbar mutane 150,000 dake gujewa fadan da akeyi da yanzu haka da nufin sake kwato birnin Mosul na kasar Iraki daga hannun 'yan ta'addan (IS).
Babban kwamishinan hukumar ta CHR, Filippo Grandi ya shaidawa manema labarai cewa komi na tafiya daidai a shirye shiryen karbar mutanen, kuma nan da kwanaki biyu ko uku hukumar zata samu runfuna 30,000 domin tsugunna da mutanen.
Yau mako guda kenan da dakarun Iraki hadin gwiwa da mayakan sa kai na 'yan Shi'a dake samun tallafin jiragen yakin kawancen da Amurka ke jagoranta suka kaddamar da wani gagarimin farmaki domin sake kwato birnin Mosul dake zamen tunga ta karshe dake hannun 'yan ta'addan IS awannan kasa ta Iraki.
MDD dai na nuna matukar damuwa dangane da halin da mutane kimanin milyan daya da rabi ke ciki yanzu haka a birnin na Mosul, saboda fadan da ake gwabzawa duk da cewa bai shafi inda mutane ke rayiwa ba sosai.
Aman saboda fargabar da ake da ita mutane kimanin milyan daya ne ke ci gaba da gujewa yankin domin tsira da rayukansu.
A halin da ake ciki dai hukumomin Iraki sun ce suna ci gaba da samun nasara a yunkurin kwato birnin na Mosul daga hannun 'yan ta'addan.