An kwato kauyuka 62 a kudancin Mosil
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i12919-an_kwato_kauyuka_62_a_kudancin_mosil
Sojojin Iraki da Dakarun sa kai sun 'yanto kauyuka 62 a kudancin Mosil daga hanun kungiyar ta'addancin nan ta IS
(last modified 2018-08-22T06:59:08+00:00 )
Oct 25, 2016 02:15 UTC
  • An kwato kauyuka 62 a kudancin Mosil

Sojojin Iraki da Dakarun sa kai sun 'yanto kauyuka 62 a kudancin Mosil daga hanun kungiyar ta'addancin nan ta IS

Tashar Telbijin din Al-Alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa daga Lokacin da Dakarun tsaron kasar Iraki suka fara kai farmaki na 'yanto garin Mosil daga 'yan ta'addar IS zuwa jiya Litinin, sun samu nasarar 'yanto kauyuka 62 dake kudancin Mosil.

A bangare guda Majiyar Dakarun hadin gwiwa na tsarkake yankin  Mosil ta fitar da rahoton  irin asarar da ta yi wa kungiyar ta'addancin IS tun daga farkon fara kai farmakin zuwa jiya Litinin.

Rahoton ya ce daga farkon fara kai farmakin 'yanto garin Mosil zuwa yanzu Dakarun tsaron kasar sun hallaka Mayakan IS 722 tare da kame wasu 23 na daban.har ila yau a yayin kai farmakin an tarwatsa  Motoci 143 na mayakan IS daga cikin su a kwai 127 dake shake da bama-bamai.

A ranar 17 ga watan Oktoba ne aka fara kai farmaki na 'yanto jihar Mosil bisa Umarnin Haidar Abadi Firaminstan kasar Iraki. Kimanin Sojojin kasar dubu 60 ne  da jami'an 'yan sanda gami da Dakarun sa kai da kuma na Kurdawa ke halartar aiyukan na tsarkake garin Mosil.

A ranar 10 ga watan yunin 2014, mayakan IS suka mamaye garin Mosil babban Jihar Nainuwa dake a matsayin babban gari na biyu a kasar Iraki.