Syria : Rasha Ta Musunta Kai Hari Kan 'Yan Makaranta
Kasar Rasha ta musunta zargin kai harin da yayi sanadin mutuwar 'yan makaranta 22 a kasar Syria, tare da yin watsi da rahoto da MDD ta fitar na zargin mahukuntan Damascos da yin amfani damakami mai guba kan al'ummar ta.
Da take bayyana hakan kakakin gwamnati Rasha, Maria Zakharova, ta ce kasar ba tada wata alaka da harin da aka kai kan makarantar ta yankin Ibled, kamar yadda wasu kafafin yada labaren kasashen yamma dana Larabawa keta yayatawa.
Dama kafin hakan kakakin ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha, Igor Konachenkov, ya ce babu inda a cikin bidiyo da jirgi mara matuki na kasar ya nuna wani hari da aka kai ta sama a yankin.
Ya kara da cewa kasashen yamma sun rufe ido akan duk irin ta'asar da akeyi a Syria a yayin da suke kumfan baki na cewa suna yaki da ta'addanci.
Al'kaluma sun nuna cewa sama da mutane 300,000 ne suka rasa rayukansu kana wasu milyoyi suka kauracewa gidajensu saboda yakin da aka shafe sama da shekaru biyar anayi a kasar Syria.