Matsin Lambar Dae'sh ( ISIS) Akan Mutanen Mosel
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13063-matsin_lambar_dae'sh_(_isis)_akan_mutanen_mosel
Kungiyar Da'esh ta kara farashin abinci a garin Mosel
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 28, 2016 15:33 UTC
  • Matsin Lambar  Dae'sh ( ISIS)  Akan Mutanen Mosel

Kungiyar Da'esh ta kara farashin abinci a garin Mosel

'Yan ta'addar kungiyar Da'esh, sun kara farashin kayan abinci a garin Mosel bayan yankewar hanyoyin kudaden shigarsu.

Cibiyar watsa labaru ta al-sumairiyyah News, ta ce; a kokarin da Da'esh ta ke yi na cike gurbin kudaden shigarta, ta kara kudaden shiga akan kayan masarufi.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Ci gaban da sojojin Iraki su ke yi na karatar birnin na Mosel, ya sa yan kungiyar ta Da'esh cikin mawuyacin hali ta fuksar tattalin arziki abinda ya sa su ke takurawa al'ummar birnin.

Sojojin Iraki dai sun kwace garuruwa da dama da su ke kewaye da birnin na Mosel.