Siriya : De Mistura, Ya Damu Da Farmakin 'Yan Tawaye A Aleppo
Wakilin musamen na MDD kan rikicin kasar Syria, ya na cikin matukar damuwa d kuma jin takaici akan hare-haren da 'yan tawayen Syria ke ci gaba da kaiwa a yammacin birnin Aleppo.
A wata sanarwa da aka fitar a Geneva, Mista Stafan de Mistura, ya ce sun samu labarin hare-hare da 'yan tawayen ke kaiwa a yankin inda fararen hula da dama galibi yara suka rasa rayukansu, baya wasu dariruwa da suka jikkata.
De Mistura ya kara da cewa babu wata hujja da wadanda ke ikirari yantar da birnin Aleppo suke da ita na farmawa birnin da irin muggan makamai haka ba kakkautawa, a inda fararen hula ke rayuwa, wanda a cewarsa ke zamen tafka laifukan yaki.
A wani share kuma De Mustura ya sake jaddada allawadai da babbansakatare na MDD Ban ki Moon yayi akan harin da aka kai kan 'yan makaranta da kuma amfani da jiragen yaki a unguwanin fararen hula.
Game da dukkan abubuwan dake faruwa a birninna Aleppo, wakilin musamen na MDD kan rikicin kasar ta Syria, Stafan de Mistura ya bayyana wajibcin tsagaita bude wuta mai daurewa a yankin.