Michel Aoun ya zama shugaban kasar Labanon
(last modified Mon, 31 Oct 2016 17:50:29 GMT )
Oct 31, 2016 17:50 UTC
  • Michel Aoun ya zama shugaban kasar Labanon

Majalisar Dokokin kasar Labanon ta zabi Michel Aoun a matsayin shugaban kasar

Tashar telbijin din Almayadin ta kasar Labanon ta habarta cewa bayan kwashe kimanin shekaru biyu da rabi ba tare da shugaban kasar ba, a wannan litinin Majalisar Dokokin kasar ta zabi Michel Aoun a matsayin sabon shugaban kasar na 13, jim kadan bayan zaben na sa , zababben shugaban kasar ya yi rantsuwa kama aiki a gaban 'yan Majalisar dokokin.

Bayan da aka sanar da zaben Michel Aoun a matsayin Shugaban kasar ta Labanon, Al'ummar kasar musaman ma na yankin Harik dake a matsayin ma'aifar sabon shugaban kasar sun bazu kan tutuna suna bayyana jin dadin su da wannan rana.

Saboda kasha landan na wasu kasashen waje a harakokin siyasar kasar ta Labanon, kasar ta kwashe shekaru biyu da rabi ba tare da Shugaban kasa ba.