Tashin Bam a babban birnin kasar Iraki.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13192-tashin_bam_a_babban_birnin_kasar_iraki.
Akalla Mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin wasu bakwai na daban suka jikkata sanadiyar tashin wasu tagwayen bama-bamai a arewa da kuma kudancin birnin Bagdaza na kasar Iraki.
(last modified 2018-08-22T11:29:10+00:00 )
Oct 31, 2016 17:50 UTC
  • Tashin Bam a babban birnin kasar Iraki.

Akalla Mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin wasu bakwai na daban suka jikkata sanadiyar tashin wasu tagwayen bama-bamai a arewa da kuma kudancin birnin Bagdaza na kasar Iraki.

Kafar watsa labaran Gad Press ta habarta cewa a wannan litinin wani Bam ya tashi a kusa da kasuwar anguwar Latifiya a kudancin Bagdaza, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutum guda tare da jikkata wasu bakwai na daban.a yankin Tarimiya ma dake arewacin birnin wani Bam na daban ya tashi da wata Motar soja inda ya kashe wani babban jami'in Soja na kasar.

A ranar lahadin da ta gabata ma wata Mota shake da bama-bamai ta tarwatse a wata kasuwa dake anguwar Huriyyat na birnin Bagdazan, lamarin da ya yi sandiyar mutuwar Mutane 8 tare da jikkata wasu sama da 30 na daban.

Bisa wani rahoto da tawagar MDD a kasar irakin da ake kira da Yunami ta fitar, birnin Bagdaza shi ne babban birni da ya fi fuskantar ta'addanci, inda a watan da ya gabata hare-haren  ta'addancin ya lashe rayukan Mutane 289 tare da raunana wasu 838 na daban a birnin.

Wannan ta'addanci dai na zuwa ne a yayin da Dakarun tsaron kasar Irakin tare da na sa kai ke ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda a kokarin da suke na tsarkake garin Mosil daga mamayar 'yan ta'addar IS.