Pakistan : Hadarin Jiragen kasa Ya Kashe Mutane 11
Rahotanni daga Pakistan na cewa mutane a kalla 11 ne suka rasa rayukansu a yayin da wasu jiragen kasa biyu sukayi taho mu gama a birnin Karashi dake kudancin kasar.
ko baya wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu da dama da suka jikkata, a daidai lokacin da masu aikin ceto ke ci gaba da kokarin zakulo wasu da suka makkale a cikin taragan jiragen.
hadarin dai ya auku ne a lokacin jirgin kasa na na Zakria Express daya fito daga lardin Multan dake birnin Pendjab a tsakiyar kasar ya ci karo da jirgin kasa na Farid Express dake tsaye a tashar Jumma Goth bayan tasowarsa daga birnin Lahore.
Kafin hakan dai wani jami'i a yankin Karashi ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa ba suda cikakun bayanai akan yawan mutanen da hadarin ya rusa dasu, aman suna da masaniya cewa adaddin fassinjojin dake cikn jiragen biyu da suka hadari zai kai dubu guda.