Farmakin Sake Kwato Garin Raqqa Na Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13504-farmakin_sake_kwato_garin_raqqa_na_siriya
Hadin gwiwar dakarun Larabawa da na Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka sun kaddamar da wani babban farmaki domin sake kwato garin raqqa na siriya cibiyar Kungiyar 'yan ta'adda IS.
(last modified 2018-08-22T06:59:12+00:00 )
Nov 07, 2016 02:25 UTC
  • Farmakin Sake Kwato Garin Raqqa Na Siriya

Hadin gwiwar dakarun Larabawa da na Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka sun kaddamar da wani babban farmaki domin sake kwato garin raqqa na siriya cibiyar Kungiyar 'yan ta'adda IS.

Dakarun na kawancen SDF wadanda suka ja dagga a garin Ain Isa da ke da nisan  kilomita 50 daga arewacin birnin na Raqqa sun yi shelar samun nasara nan ba da dewa ba.

Yau kusan shekaru biyu da rabi kenan da birnin Raqqa na Siriya ke cikin hannun Kungiyar IS.

Wannan farmakin na zuwa ne a daidai lokcin da ake kokarin korar 'yan ta'addar na IS daga wacen tungarsu da ke a birnin Mosul na Iraki.

Gariruwan Mosul da Raqqa wadanda keda tazara kilomita 400 tsakaninsu na zamen birane biyu mafi girma da kungiyar IS ke rikeda.

Saidai a farmakin da take sha a baya bayan nan daga dakarun kasar Iraki kungiyar ta rasa wurare da dama a birnin Mosul.

Amurka wace ke goyan bayan dakarun ta bakin sakataren tsaron ta Ashton Carter ta bayyana cewa za'a sha wahala a yakin, aman za'a iya karya laggon kungiyar akan shirye shiryen ta na kai hare haren ta'addanci a Amurka.

Tun dai bayan da kawancen ya soma kai farmaki da yammacin ranar Asabar data gabata ya yi nasara kwato kauyuka da dama a wannan jiya dake arewacin kasar Syria.

Mme Jihan Cheikh Ahmad kakakin kawacen ta shaida cewa zasu nasara a wanna yakin kamar yadda ta kasance a Kobane, Tall Abyad, Hassake, Al-Hol, Chaddade da Minbej biranen da aka sake kwatowa daga hannun 'yan ta'addan IS a 'yan watanni nan.

A gefe guda kuma a cen Irakin inda ake ci gaba da kai farmaki kan 'yan ta'addan na IS Firaministan kasar, Haider al-Abadi ya sha alwashin kawo karshen kungiyar da kuma kwato garin Mosul.

Mista al-Abadi wanda ke bayyana hakan a wata ziyara da ya kai a wasu yankunan da suke kusa da garin na Mosul inda ya je don isar da sako ga mutanen garin dake shan ukubar kungiyar.

Firayi ministan Al-Abadi ya bayyana jin dadinsa da yadda ake ci gaba da samun nasarori a kan 'yan ta'addan na Da'esh wanda ya ce nasarorin da ake samu din ya ma dara yadda aka yi tsammani kafin fara kaddadamar da hare-haren kwato garin.

A ranar 17 ga watan Oktoban da ya  gabata ne dai sojojin Irakin tare da hadin gwiwan dakarun sa kai  suka  kaddamar da gaggarimun farmakin sake kwato garin na Mosul daga hannun 'yan ta'addan wadanda suke rike da shi tun sama da shekaru biyu da suka gabata.