Manufofin Hare-Haren Ta'addancin Baya-Bayan Nan A Kasar Iraki
(last modified Tue, 08 Nov 2016 05:48:45 GMT )
Nov 08, 2016 05:48 UTC
  • Manufofin Hare-Haren Ta'addancin Baya-Bayan Nan A Kasar Iraki

Rahotanni daga kasar Iraki sun bayyana cewar shugaban kasar Fu'ad Ma'asum ya sha alwashin cewa jinin mutanen da aka zubar sakamakon wani harin ta'addancin da aka kai garin Samarrah a kasar a ranar Lahadin da ta gabata ba zai tafi haka kawai ba tare da daukar fansa a kan 'yan ta'addan da suka kai harin ba; kamar yadda kuma ya kirayi hukumomin tsaron kasar da su dau matakan da suka dace wajen kawo karshen irin wadannan hare-haren ta'addanci.

A yayin wannan hari na ta'addanci da aka kai birnin na Samarra a ranar Lahadin da ta gabata a wani wajen ajiyar motoci na haramin Imaman Shi'a guda biyu wato Imam Hadi da dansa Imam Askari (a.s) da ke ganin na Samarrah, wasu 'yan Iran su 8 da suka kai ziyara wajen ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 102 kuma suka sami raunuka.

Har ila yau a cikin 'yan kwanakin nan din ne dai wasu mutane 14 suka rasa rayukansu kana wasu 25 kuma suka sami raunuka a wani harin ta'addanci da aka kai garin Tikrit na lardin Salahudden na kasar Irakin. Kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) ta dauki alhakin kai dukkanin wadannan hare-hare guda biyu.

Tun dai bayan kaddamar da hare-haren da 'yanto garin Mosil daga hannun 'yan ta'addan Da'esh din da gwamnatin Irakin  ta kaddamar da kuma shan kashin da 'yan ta'addan suke yi ya sanya su kara yawan hare-haren ta'addancin da suke yi da zubar da jinin fararen hulan da ba su ci ba su sha ba.

Masana harkokin siyasa sun ganin karin kaimin da 'yan ta'addan suka yi cikin kwanakin nan wani kokari ne na dushe haske wasu batutuwa masu muhimnmanci da suke kan hanyar faruwa a Irakin, su ne kuwa: gagarumin jerin gwanon Arba'in na Imam Husain (a.s) da kuma bukukuwan nasarar kwato garin Mosil wanda ake ganinsa a matsayin bugun karshe ga kasantuwar 'yan ta'addan Da'esh din a kasar Irakin.

A saboda haka ne a kokarin 'yan ta'addan na kawar da hankulan mutane daga irin kashin da suke sha a hannun sojoji da dakarun sai kai na Irakin, haka nan kuma da sanya tsoro da fargaba a zukatan al'umma da kuma tilasta wa gwamnatin kasar dakatar da wannan shiri na kwaro garin na Mosil, ya sa suka kara kaimin irin wadannan hare-hare da suke kai wa.

A bangare guda kuma sakamakon irin damuwar da 'yan ta'addan suke ciki kan duk wani taro da zai wayar da kan al'ummar musulmi dangane da irin danyen aikin da suke yi; don haka suke tsananin adawa da tarurruka irin na arba'in wanda zai gabatar da addinin Musulunci yadda yake da kuma kunce wa makiya da 'yan amshin shatansu irin su Da'esh din da babu abin da suka sa gaba in ban da shafa kashin kaji ga wannan addini na Musulunci.

A wannan shekara ma dai kamar shekarun da suka gabata tuni al'ummomin musulmi da suka fito daga sama da kasashe 60 na duniya suka fara isa wasu kuma suna hanyar isa garin Karbala na kasar  Iraki da nufin shiga cikin bukukuwan kwana arba'in na shahadar Imam Husain (a.s). Ko shakka babu taron Arba'in wata bayyananniyar alama ce da ke nuni da hadin kan Shi'a-Sunna wajen tinkarar bakar akidar wahabiyawa 'yan takfiriyya masu aikata wannan aiki na ta'addanci.

Don haka ne da dama suke garin wannan gagarumin taron na miliyoyin musulmi wani lamari ne da ke nuni da shan kashin akidar wuce gona da iri da kuma masu bakar aniya ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar Irakin da ma sauran kasashen musulmi

Ko shakka babu, bisa la'akari da yadda sakon Imam Husain (a.s) ya zamanto wani sako ne na kasa da kasa da bai takaita ga wani yanki ba, don haka gudanar da jerin gwanon Arba'in din yana nuni da irin ci gaban da al'ummar musulmi suka samu ne a tafarkin su na tabbatar da gaskiya da kuma fada da zalunci da girman kan duniya, lamarin da 'yan ta'addan da masu kafirta musulmin ba sa so.