Sojojin Siriya Sun Harbo Jirage Marasa Matuka Na 'Yan Ta'adda 14
Sojojin Siriya da dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar kakkabo jiragen sama marasa matuka guda 14 da 'yan ta'addan kasar suke amfani da su a lardin Dara'a da ke kudu maso yammacin kasar ta Siriya.
Kafafen watsa labarai sun jiyo wata majiyar sojin kasar Siriyan tana fadin cewa sojojin Siriya da dakarun sa kai masu goya musu baya sun kakkabo wadannan jiragen ne a daidai lokacin da suke gudanar da ayyukan leken asiri da tattaro bayanan sirri da kuma kokarin kai hare-hare kan wasu sansanoni na sojojin Siriyan.
A wani bangaren kuma sojojin kasar Siriyan sun sami nasarar hallaka wani adadi na 'yan ta'addan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhat Fateh al-Sham da a da ake kira da Al-Nusra Front da kuma raunana wasu da dama bugu da kari kan lalata musu makamansu sakamakon wani ba ta kashi da ya gudana tsakanin bangarori biyu
Kamar yadda kuma sojojin Siriyan sun sami nasarar dakile wani shiri dna 'yan ta'addan na kai hare-hare kan wasu sansanonin sojin kasar a gabashin yankin Hadir da ke lardin Quneitra, inda suka kashe 'yan ta'addan da kuma kace musu makamai.
Sojojin Siriyan dai suna ci gaba da samun nasararori a kan 'yan ta'adda da wasu kasashe suka shigo da su kasar daga wasu kasashe daban-daban na duniya da nufin dagula lamurra a kasar Siriya.