Harin Ta'addanci A garin Halab Na Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13816-harin_ta'addanci_a_garin_halab_na_syria
Fararen Hula Da Dama Sun mutu Yayin da Wasu suka jikkata A Harin 'Yan ta'adda A Garin Halab
(last modified 2018-08-22T06:59:14+00:00 )
Nov 13, 2016 08:37 UTC
  • Harin Ta'addanci A garin Halab Na Syria

Fararen Hula Da Dama Sun mutu Yayin da Wasu suka jikkata A Harin 'Yan ta'adda A Garin Halab

"Yan ta'adda a kasar Syria sun kai hari akan birnin Halab, ta hanyar harba manyan bindigogi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da  kuma jikkata wasu.

Harin na jiya asabar an kai shi ne dai a gidajen mutane da ke yankin yammacin birnin, Kawo ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane uku da kuma jikkatar wasu 15. Bugu da kari gidajen mutane da dama sun rushe.

Tun bayan da 'yan ta'addan da ke cikin birnin na Halab, su ka kasa yin fito na fito da sojojin kasar, sun koma kai wa fararen hula hari.