IS na ci gaba da kisan fararen hula a gabashin Mausil
Mayakan ISIS sun kashe fararen hula da dama a gabashin garin Mausil
A wata sanarwa da Dakarun kasar Iraki suka fitar a wannan Alkhamis, Akalla Mutane 31 suka rasu sanadiyar wani mumunar hari da mayakan ISIS suka kai kan gidajen fararen hula a gabashin garin Mausil na jihar Nainuwa, 7 daga cikim su kananen yara ne. baya ga hakan mayakan na ISIS sun rusa wani babban masallaci a yankin Al-Akha'a na gabashin garin Mausil.
A bangare guda Dakarun Iraki sun samu nasarar tsarkake wani kauye dake gudancin garin na Mausil a wannan Alkhamis.har ila yau Jiragen yakin kasar sun yi ruwan bama-bami kan maboyar 'yan ta'addar na ISIS a yankin Ashakaku Khadara'a daga gabashin garin na Mausil.
Tun a ranar 17 ga watan Oktoban da ya gabata ne Dakarun tsaron Iraki tare da Dakarun sa kai suka fara kai farmaki kan 'yan ta'addar IS da nufin 'yanto shi daga mamayar 'yan ta'addar, kuma a halin da ake ciki Dakarun musaman na yaki da ta'addanci sun samu nasarar korar 'yan ta'addar IS din a wani bangare na garin Mausil da suka mamaye shi tun a shekarar 2014.