Iraki : Mutane 33 Ne Suka Rasu A Harin Ta'adancin ISIS
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1441-iraki_mutane_33_ne_suka_rasu_a_harin_ta'adancin_isis
Rahotanni daga kasar Iraki na cewa akalla mutane 33 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta'adanci da kungiyar (IS) ta dauki alhakin kaiwa a wata kasuwa da ke unguwar 'yan Shi'a a birnin Bagadaza.
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 29, 2016 02:44 UTC
  • Iraki : Mutane 33 Ne Suka Rasu A Harin Ta'adancin ISIS

Rahotanni daga kasar Iraki na cewa akalla mutane 33 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta'adanci da kungiyar (IS) ta dauki alhakin kaiwa a wata kasuwa da ke unguwar 'yan Shi'a a birnin Bagadaza.

Harin wanda aka kai a unguwar Sadr City, wanda ke zaman mafi muni cikin wannan shekara a birnin na Bagadaza, ya kuma jikatta wasu mutane 79.

Majiyoyin tsaro dana lafiya a wannan kasa sun shaida wa masu aiko da rahotanni cewa 'yan ta'adan sun kuma kai hari a wani shingen soji da ke yammacin birnin na Bagadaza inda suka kuma kashe wasu jam'ian tsaro takwas tare da jikkata wasu 22.

A kasar Iraki dai 'yan ta'ada dake ikirari da sunan jihadi na amfani da wannan salo na kai hare-haren kunar bakin wake a wuraren wadanda basu ji basu gani ba.

ko a ranar Alhamis data gabata ma wasu hare-hare kunar bakin wake kan wuraren ibadun 'yan shi'a a birnin Bagadaza sun yi sanadin mutuwar mutane tara tare da jikkata wani adadi.