An kai harin Ta'addanci a birnin Bagdaza na kasar Iraki
Akalla Mutane biyu ne suka rasa rayukan su sanadiyar wani harin ta'addanci a birnin Bagdaza na kasar Iraki
A wata sanarwa da Sa'ad Mu'in Kakakin jami'an 'yan sanda na birnin Bagdaza ya sanar Akalla fararen hula biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 7 na daban suka jikkata sanadiyar tashin wata Mota shake da bama-bamai jiya Litinin a kusa da wani dandali na sayar da kayen ganye dake gabashin birnin na Bagdaza.ko bayan ga hakan rahoton ya ce Motoci da kuma shagunan Mutane da dama ne suka kama da wuta sanadiyar tashin bam din.
A bangare guda, Dakarun sa kai na kasar Irakin sun samu nasarar tsarkake kauyuka hudu da suka hada da Kauyen Maflakatu Junubi, Turkumaniya Junubi, Turkumaniya Shimali da Assalam dake gudancin tal'afar na gudancin garin Mausil daga kalkashin mamayar 'yan ta'addar IS tare da ceto dariruwan fararen hula daga kangin rayuwa na bakin milkin kama karyar kungiyar ta ISIS.
Har ila yau Dakarun sa kai din sun samu nasarar fatattar 'yan ta'adda daga babbar hanyar da ta hada garin Tal'afar da garin Atabat tare kuma da yanke duk wata sadarwa tsakanin 'yan ta'addar na garin Tal'afar da garin Hadar,inda aka hallaka 'yan ta'addar IS din da dama.